Shugaban kwamitin tsaro a lardin Zi-qar na kasar Iraki Jabbar Musawi a jiya Lahadi ya bayyana cewar Hukumar leken asirin kasar Iraki ta tabbatar da labarain cewa; akwai tarin ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai kimanin 3,000 da suke neman hanyar kutsa kai cikin kasar Iraki daga yankunan sahara na Samawa, Nasiriyya da Wadil-Khak da suke iyaka da kasar Saudiyya da nufin kai dauki ga mayakan kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham da suka mamaye wasu garuruwan kasar Iraki makonni biyu da suka gabata.
Musawi ya kara da cewar a halin yanzu haka jami’an tsaron Iraki suna cikin shirin ko-ta kwana domin kalubalantar duk wani kutsen ‘yan ta’adda zuwa cikin kasar ta Iraki domin gudanar da ayyukan ta’addanci. A ‘yan kwanakin baya bayan nan majiyar tsaron Iraki ta watsa labarin cewa; jami’an leken asirin kasar Saudiyya kimanin 150 ne suka shiga cikin kasar Iraki domin tallafa wa ayyukan ta’addanci a yankunan da kungiyar daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish ta mamaye.